Kotu a Faransa ta sake bayar da sammacin kamo mata tsohon shugaban Syria

Kotu a Faransa ta sake bayar da sammacin kamo mata tsohon shugaban Syria

 

An bayar da wannan umarni ne a wani bangare na bincike kan lamarin Salah Abou Nabour, wanda ke da shaidar dan kasar Faransa da kuma Syria da aka kashe a ranar 7 ga watan Yunin 2017 a wani harin bam da aka kai a Syria.

Wannan shi ne sammacin kamo hambararren shugaban karo na biyu da alkalan Faransa suka bayar, wanda dakarun ‘yan tawaye karkashin jagorancin kungiyar Hayat Tahrir al-Sham suka sauke a farkon watan Disamban bara.

A watan Nuwamban 2023, mahukuntan Faransa suka bayar da sammacin farko na a kamo Bashar al-Assad, bisa zarginsa da hannu a laifuffukan cin zarafin bil adama da kuma hada kai wajen aikata laifukan yaki.

Hakan ya biyo bayan wani bincike da Faransa ta gudanar kan yadda aka gudanar da wasu hare-hare masu dauke da guba a Douma da gundumar Ghouta da ke Gabashin kasar a watan Agustan 2013 wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 1,000.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)