Korona za ta zama tarihi karshen bazarar bana

Korona za ta zama tarihi karshen bazarar bana

Kwararru a harkokin kiwon lafiya a kasar Turkiyya sun bayyana cewa komai zai koma dai-dai a karshen bazara yayinda kwayar cutar Korona ke cigaba da zama kalubale ga harkokin yau da kullum a fadin duniya.

Dr. Mustafa Necmi Ilhan, shugaban sashen lafiya a jami’ar Gazi dake babban birnin Turkiyya, Ankara da kuma mamba a Hukumar Kiwon Lafiya a Kasar Turkiyya Dkt. Mustafa Centiner sun yi sharhi akan matsalolin da Korona ke haifarwa.

A yayinda suke bayyana cewa babu takamaimen lokacin da za’a bayyana cewa za’a kawo karshen Korona, Ilhan ya bayyana cewa ganin yadda ake bin dokokin da aka sanya domin yaki da cutar da kuma samar da allurar riga-kafi da aka yi za’a iya bayyana cewa akwai fata mai kyau ga Turkiyya ga ma duniya baki daya.

Sabili da haka ga dukkan alamu za’a iya kawo karshen annobar a karshen bazarar shekarar bana.


News Source:   ()