Korona ta yi kamari a cikin dabbobin gida

Korona ta yi kamari a cikin dabbobin gida

Sabon nau'in cutar coronavirus (Kovid-19) ya kasance ruwan dare a cikin kuliyoyi da karnukan da masu su suka kamu.

A labarin da BBC ta rawaito, masana daga jami'ar Utrecht da ke Netherlands sun yi gwajin jini a kan kuliyoyi da karnuka da ke gida daya da mutanen da suka kamu da Kovid-19.

A cikin tsarin binciken, an gwada dabbobi 310 a cikin gidaje 196 inda mutanen da suka kamu da Kovid-19 a kwanaki 200 da suka gabata suke.

Sakamakon gwajin kuliyoyi 6 da karnuka 7 ya tabbatar da cewa suna dauke da kwayar cutar, kuma an gano cewa dabbobi 54 sun samar da kwayoyin kariya daga Kovid-19.

An bayyana cewa yawancin kuliyoyin da karnukan da suka kamu da cutar basu nuna wata alama ba ko kuma alamomin da suka nuna basu bayyana sosai ba.

Wani binciken da Jami'ar Guelph da ke Kanada ta gudanar ya nuna cewa kuliyoyin da ke kwana akan gado tare da masu su suna cikin hadarin kamuwa da cutar ta Covid-19.

A tsakanin binciken, kuliyoyi 48 da karnuka 54 daga gidaje 77 aka bincika akan ko sun samu kariya daga kwayoyin cutar Kovid-19; kuma an tambayi masu su ko suna huldan kud-da-kud da dabbobinsu.

A yayinda sakamakon gwajin na kashi 67 cikin dari na kuliyoyin, kashi 43 cikin dari na karnuka sun tabbatar da suan dauke da Korona, a wannan kiyasin an gano kashi 3 cikin dari na kuliyoyin kan titi da kuma kashi 9 na karnukan kan titi dauke da cutar Korona a yankin.

Yayinda kashi daya cikin hudu na dabbobin gida ke nuna alamun cutar Kovid-19 kamar wahalar numfashi, an lura da karin hadarin kamuwa da cutar a cikin kuliyoyin dake kwana kusa da fuskokin masu su.


News Source:   ()