Korona ta yi ajalin mutum miliyan 1 da dubu 682 a doron kasa

Korona ta yi ajalin mutum miliyan 1 da dubu 682 a doron kasa

A fadin duniya kawo yanzu kwayar cutar Covid-19 tayi sanadiyar rayukan mutum miliyan 1 da dubu 682, inda yawan wadanda suka kamu da cutar ya kai miliyan 76 da dubu 81, yawan wandanda suka warke kuma ya kai miliyan 53 da dubu 341.

A kasar Indiya Corona ta yi ajalin mutum dubu 145 da dari 178, yawan wadanda suka kamu da ita kuwa sun kai miliyan 10 da dubu 5 da dari 850.

A Nahiyar Afirka annobar ta yi ajalin mutane dubu 58 da dari 407, haka kuma da karin kama mutum dubu 19 da 335 yawan wadanda suka kamu da cutar a jumlace sun kai miliyan 2 da dubu 483 da dari 520. A nahiyar a kasar Afirka ta Kudu ce cutar ta fi yin kamari inda mutum dubu 24 da dari 285 suka rasa rayukansu. Sai kuma Misira inda cutar ta yi ajalin mutum dubu 6 da dari 854 da kuma Morocco na binsu a baya a matsayar ta uku da cutar korona ta fi yin illa a Afirka inda mutum dubu 6 da dari 854 suka rasa rayukansu.

A kasar Mali kuwa inda aka samu mutuwar mutum 215 sanadiyar cutar da kuma samun masu dauke da ita har dubu 6 da dari 120 an kaddamar da dokar ta baci na kwanaki 10, dokar ta sanya rufe makarantu da gidajen siyar da abinci.

 


News Source:   ()