Ma’aikatar Lafiyar kasar Jordan ta sanar da cewa annobar Korona ta yi ajalin karin mutum 96 da kuma kama karin mutum dubu 8, 433 a kasar.
Kawo yanzu dai yawan wadanda Korona ta kama a kasar sun kai dubu 571,290 da kuma sanadiyar rayukan dubu 6,277 a fadin kasar.
Haka kuma mutum dubu 463,893 sun warke daga cutar a fadin kasar.
A halin yanzu dai Jordan na fuskantar barkewar annobar a karoi na biyuy inda yawan wadanda ke mutuwa a rana ya haura mutum 100.