Annobar Covid-19 ta sanya dakatar da tattuanwar da ake yi domin cimma matsaya akan Brezit tsakanin Tarayyar Turai da kasar Birtaniya.
Kamar yadda jagoran tattaunawar a bangaren tarayyar Michel Barnier ya yada a shafukansa na sadar da zumunta an dakatar da tattaunawa akan yarjejeniyar kasuwanci da kuma yadda hulda zata kasance tsakanin bangarorin biyu.
Barnier ya kara da cewa,
"Daga cikin masu tattaunawar an samu mutum daya dauke da Covid-19. Tare da shugaban yarjejeniyar a bangaren Birtaniya David Forst mun amince mu dakatar da zaman zuwa wani lokaci"
Frost, ya yada a shafinsa na sadar da zumunta da cewa, muna ci gaba da tattaunawa da Michel Bernier, abu mai muhinmanci na farko shi ne lafiyarmu, muna masu godiya ga irin gudunmowar gaggawa da tarayyara Turai ta bamu