Hukumar kididdigar kasar Turkiyya ta sanar da cewa an samu raguwar auratayya a cikin shekarar 2020 a kasar lamarin da aka ta’alaka a matsayin daya daga cikin matsalolin da Korona ke haifarwa a doron kasa.
Hukumar ta bayyana cewa an samu raguwar dauren aure da kaso 10.1 cikin dari da kuma raguwar saki da kaso 13.8 cikin dari a cikin shekarar 2020 lamarin da aka bayyana cewa ya faru ne sabili da dage ranakun dauren aure da ma’aurata suka dinga yi sabili da Korona.
Raguwar saki kuwa nada nasaba ne ga yadda Korona ta sanya ma’aurata kasancewa kusa da juna sabili da dokar hana fita waje da aka rinka sakawa a kasar.
Kamar yadda jaridar Daily Sabah ta rawaito Dkt. Kafali ya bayyana cewea a fadin duniya ma Korona ta haifar da raguwar daurin aure. A Japan a shekarar 2020 yawan auren da ake daurawa ya ragu da kaso 12.7 cikin dari wanda ba’a taba samun raguwa kamar haka bat un daga shekarar 1950. A Italiya hukumar kididdigar kasar ta sanar da cewa yawan auratayyan ya ragu a cikin watanni hudun farkon shekarar 2020 da kaso 20 cikin dari idan aka kwatanta da na 2019. Haka kuma raguwar ya karu zuwa kaso 80 cikin dari a cikin watanni hudu kaso na biyun shekarar 2020 inda kuma yawan sake-sake ya ragu da kaso 60 cikin dari.