Annobar Korona baya ga matsalolin da take haifarwa ta kuma kara haifar da matsalar jana'iza a kasar Italiya.
Jaridun Italiya sun ba da sanarwar cewa an jirkintar da yin dubban jana'iza na tsawon watanni.
Wani dan majalisar dokoki a Italiya ya bayyana cewa, bayan rasuwar dansa ba'a binne shi ba har tsawon watanni biyu.
An bayyana afkuwar matsalolin akan rashin tsarin gwamnati da kuma gurbatattun gidajen wanke gawa dake kasar.
A halin yanzu dai ana ikirarin cewa babu sauran wuri a makabartu a wasu yankuna a kasar.
Yawan gawawwakin da ba za'a iya binne su ba a cikin babban birnin Rome kawai ya karu zuwa dubu 2.
An ajiye wasu daga cikin gawarwakin a cikin makabartar a arewacin birnin ba tare da an binnesu ba.
Kasancewar kamuwa da kwayar cutar corona da ma’aikatan jana’izar suka yi ya kara dagule harkokin jana'izza a fadin kasar.
An kuma yi ikirarin cewa dakunan wanke gawawwakin ba za su iya wadata ko ci gaba da aiki ba saboda karuwar asarar rayuka a wannan watan.