An sanar da cewa yawan wadanda ke kashe kansu sun karu a Japan sabili da matsalolin yau da kullum da Korona ke cigaba da haifarwa a doron kasa.
Ma’aikatar Lafiyar kasar ce ta sanar da cewa yawan wadanda suka kashe kansu ya kai dubu 20,919 a cikin shekarar 2020 wanda ke nuna karin kaso 3.7 cikin dari idan aka kwatanta dana shekarar baya.
A cikin wannan lokacin Korona dai, duk da kasancewarta annoba ta yi ajalin mutum dubu 3,460 ne a Japan kasa da yawan wadanda suka kashe kansu.
An tabbatar da cewa karin da aka samu na kisan kai a shekarar ta 2020 a kasar Japan ba’a taba samu irinsa a cikin shekaru goma da suka gabata ba.