Bincike ya nuna cewa a yanayin annobar Korona da ake ciki ta haıfar da haihuwar jarirai a mace da kuma mutuwar mata sanadiyar nakuda ya karu da kaso daya bisa uku a fadin duniya.
Cibiyar Binciken Harkokin Kiwon lafiya ta Lancet Global Health a bincike 40 da ta yi a kasashe 17 ta gano cewa sabili da saka dokar hana fita waje masu juna biyu sun rage zuwa asibiti lamarin da ya haifar da matsaloli garesu.
A sabili da haka an samu karuwar haihuwar jinjirai ba rai, mutuwar mata a nakuda da kuma tabarbarewar lafiyar mata masu jego da kusan kaso daya bisa uku.
Ferfesa Asma Khalil dake jami'ar St George dake birnin Landan ta bayyana cewa,
"Covid-19 ta haifar da kalubale mai girma a fannonin lamurran kiwon lafiya. Musanman a kasashe masu tasowa da matsakaita karfi annobar ta fı haifar da karin yawan mutuwar mata a nakuda da ma rasa jariran da ake haihuwa."