Annobar COVID-19 ta haifar da hasarar zunzurutun kudi har dala tiriliyon 1.3 a fannonin yawon bude ido tsakanin kasa da kasa a cikin shekarar 2020.
Raguwar yawan tafiye-tafiye a cikin shekarar ne ya haifar da hasarar abinda Majalisar Dinkin Duniya ta kira shekara mafi muni a fannin yawon bude ido.
Kungiyar Hada-hadar Yawon Bude Ido dake Madrid wato WTO ce ta bayyana cewa an samu raguwar samun kudaden shiga a fannonin yawon bude sau 11 idan aka kwatanta dana shekarar 2009 da aka samu raguwar sabili da tabarbarewar tattalin arziki.
Kungiyar WTO ta bayyana cewa kimanin ma’aikata miliyan 100 zuwa 120 ka iya rasa aikinsu sabili da tabarbarewar fannin yawon bude ido a doron kasa.
Harkokin yawun bude ido ya sauka da kaso 74 cikin dari a shekarar 2020 sabili da Korona inda yankin Asiya tafi fuskantar matsalar.