Korona ta fi yakin duniya na biyu tayar da hankalin al'umma

Korona ta fi yakin duniya na biyu tayar da hankalin al'umma

Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya wato WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya bayyana cewa "mummunan tashin hankalin" da sabon nau'in kwayar cutar coronavirus ya haihar  ya fi na Yakin Duniya na Biyu.

Dangane ga Sputnik bayanin da Ghebreyesus ya yi,

"Al'umma da dama sun kasance cikin tashin hankali a yakin duniya na biyu. Amma annobar Korona ta fi tayar da hankalin al'umma fi ye da na yakin duniya na biyu"

Ghebreyesus, ya kara da cewa tashin hankalin da Korona ta haifar zai jima ga zukatan al'umma a doron kasa.

Maria Van Kerkhove, wata masaniya lafiyar kwakwalwa  daga WHO, ta jaddada cewa, ya kamata lafiyar kwakwalwa ta mutane ta zama fifiko kuma ta yi gargadin cewa wacanan annoba za ta yi matukar tasiri ga halayyar dan adam a cikin dogon lokaci.

 


News Source:   ()