Korona ka iya kara yaduwa a doron kasa

Korona ka iya kara yaduwa a doron kasa

Ministan Kiwon Lafiyar kasar Jamus Jens Spahn ya yi gargadin cewa ana iya samun karuwan masu kamuwa da kwayar cutar Korona sosai a watanni masu zuwa.

Spahn a wani taron manema labarai a Berlin babban birnin kasar ya yi nuni da cewa an samu karuwar masu kamuwa da Kovid-19 a cikin ‘yan kwanakin nan.

Da yake bayyana cewa yawan masu kamauwa da Kovid-19 da ake gani a cikin mutane dubu 100 a kowane mako a halin yanzu yana kusa da 11, ya kara da cewa,

"Idan wannan adadin ya ninka duk bayan kwanaki 12 kamar yadda yake ninkawa a yanzu, zai wuce 400 a watan Satumba da 800 a watan Oktoba." 

Minista Spahn ya bayyana cewa ya kamata kowa ya tambayi kansa ko za'a yi wannan sakacin ko a'a, sannan ya bukaci jama'a su bi matakan da aka bayyana don hana yaduwar cutar.

Da yake bayanin cewa yana da mahimmanci a sanya takunkuma rufe fuska, ya kara nuni ga muhinmancin yin allurar riga-kafin Korona.
A cikin wannan watan na Yuli ne ya kamata mu shiryawa yadda lamurran Korona zasu kasance a watannin Satumba, Oktoba, da Nuwamba.
 


News Source:   ()