An kaddamar da dokar ta baci a jihohin Hokkaido, Okayama da Hiroshima dake kasar Japan sanadiyar karin yawan wadanda suka kamu da sabuwar kwayar cutar Coronavirus (Kovid-19).
Ya zuwa safiyar jiya, jihohin Hokkaido, Okayama da Hiroshima sun kasance cikin yanayin dokar ta baci, wanda a halin yanzu ke gudana a jihohin Tokyo, Kyoto, Hyogo, Osaka, Aichi da Fukuoka.
Don haka, an fadada girman dokar ta baci a fadin kasar zuwa jihohi 9.
Dokar ta bacin a dukkan yankuna za ta kare ne a ranar 31 ga watan Mayu.