Koriya ta Kudu ta sanar da kaddamar da mataki mafi tsauri a yaki da COVID-19 bayan da kasar ta ba da rahoton sama da mutane 1,300 da suka kamu da cutar, wanda shi ne mafi girma a rana guda tun bayan barkewar cutar, a cewar kafofin yada labarai na cikin gida.
Tsauraran matakan akan yaki da Korona za su fara aiki daga Litinin zuwa makonni biyu a babban birnin Seoul, lardin Gyeonggi da ke kusa da shi da kuma Incheon tashar jiragen ruwa ta yamma, in ji kanfanin dillancin labaran Yonhap News Agency.
Duk cibiyoyin nishadi, gami da wuraren shakatawa na dare, za a rufe su, yayin da za a bar gidajen abinci su rika aiki har zuwa 10 na dare.
An kuma hana taron mutane uku ko fiye da haka kuma an sanya dokar hana fitar dare bayan karfe 10.
Sabon takunkumin ya zo ne bayan da kasar ta ba da rahoton mutane dubu 1,316 sun kamu da cutar a cikin awanni 24 da suka gabata, wanda shi ne adadi mafi yawa na yau da kullum tun lokacin da cutar ta addabi Koriya ta Kudu a bara a watan Janairu.
Ya zuwa yanzu, Koriya ta Kudu ta yi rajistar mutane dubu 164,028 da suka kamu da cutar tare da mutuwar 2,036, a cewar Hukumar Kula da Rigakafin Cututtukan Koriya.