An sanar da cewa Koriya ta Arewa ta babbake wani ofishin hulda tsakaninta da Koriya ta Kudu.
Ma'aikatar Hadakar kasahsen dake Koriya ta Kudu ta sanar da cewa ofishin huldan da aka rushe na a garin Kaesong ne a Koriya ta Arewa.
A baya dai gwamnatin Pyonyang ta yi barazanar cewa zata rufe ofishin hulda tsakaninta da gwamnatin Seoul bayan tashin hankali da ya kara kamari tsakanin kasashen biyu a lokacin da masu fafutuka a Koriya ta Kudu suka aike da takarda zuwa ga Koriya ta Arewa.
Wasu masana sun bayyana cewa sanadiyar takunkuman da Amurka ta kakkabawa Koriya ta Arewa, Koriya ta Kudu ta dakatar da wasu huldan kasuwanci tsakaninta da ta Arewa lamarin da bai yiwa Koriya ta Arewar dadi ba.
Bayan lamurka sun kara kamari tsakanin kasashen biyu dakarun Koriya ta Arewa sun kara kaimi tare da nuna barazana a iyakokin kasarssu da Koriya ta Kudu.