Koriya ta Arewa ta fitar da sabbin makamai masu linzami da ba'a taba ganin irinsu ba

Koriya ta Arewa ta fitar da sabbin makamai masu linzami da ba'a taba ganin irinsu ba

Kasar Koriya ta Arewa ta nuna sabbin makamai masu linzami a bikin zagayiowar kafuwar jamiyyar ma'aikata ta shekara 75.

A bikin cikan shekara ta 75 da kafuwar jamiyyar ma'aikata da aka gudanar a babban birnin ķasar Pyongyang aka baje kolin sabbin makamai masu linzami na ķasa da ķasa. 

Daga cikin sabbin makamai masu linzami na ķasa da ķasa da Koriya ta Arewar ta baje an lura da sanfarin  Pukguksong 4-A wanda ba'a taba ganin irinsa a doron kasa ba.

A taron da shugaban Koriya ta Arewar Kim Jong-un, ya yi jawabi ya bayyana cewa kasarsa ba'a taba samun wanda ya kamu da kwayar cutar corona ba sabili da hakan ne muka kasance masu godiya.

A yayinda Kim Jong-un, ke nuna bakin cikinsa da yadda korona ke addabar duniya ya yi fatar samun sauki cikin gaggawa ga dukkanin alumman dake fama da cutar corona  a fadin duniya.


News Source:   ()