Hukumar leƙen asirin Koriya ta Kudu ce ta tabbatar da aikewa da dakarun sojin masu tarin yawa zuwa Rasha domin taimakawa Mascow a yaƙin da take gwabzawa da Ukraine.
Dama rahotanni hukumar sun tabbatar da cewa akwai dakarun Koriya ta Arewa na musamman 1500 dake Rasha da suke karbar horo na musamman.
Hukumar leƙen asirin ta saki wasu hotunan tauraron ɗan adam dake nuna kason farko na sojin Koriya ta Arewa na nufar wani sansanin sojin Rasha dake Vladivostok.
Ta ce a ranar 8 da 13 ga watan Octoba na wannan shekara ta gano yadda ƙasar ta yi jigilar dakarun soji zuwa Rasha a cikin wani jirgin ruwan Mascow, inda hakan yake ƙara tabbatar da shigar Koriya ta arewa yakin dumu-dumu.
Sojin da aka aike na musamman an zabosu ne daga cikin wata tawagar ƙwararrun mayakan Koriya ta arewa, kuma sojin za su shiga yaƙin ne domin fafatawa da zarar sun kammala karbar horon da ya kamata.
Hukumar leken asirin Koriya ta Kudu ta ce akwai yuwuwar Koriya ta Arewa za ta aike da dakarun soji da yawansu ya kai dubu 12, ana kuma sa ran za a yi jigilar kaso na 2 na sojin ba da jimawa ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI