Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-un ya yi gargadin cewa yanayin karancin abinci a kasar "abin damuwa ne"
Da yake magana a wajen taron kolin kwamitin kolin Jam’iyyar Workers Party mai mulkin kasar, Kim ya yi kira da a tattauna da kasashen duniya kan yadda Koriya ta Arewa za ta tunkari “yanayinta da halinta tsakanin kasashe "
Kim bai fito fili ya ambaci Amurka da makwabciyarta ta Kudu a cikin kiran nasa ba amma,
Tare da jaddada cewa matakan dakile sabuwar nau'in cutar coronavirus (Kovid-19) da bala'in ambaliyar ruwa a duk cikin shekarar 2020 ya shafi tattalin arziki, Kim yayi gargadi game da karancin abinci.
Kim ya ce yanayin abinci a kasar "abin damuwa ne" don haka ya bukaci hukumomi su dauki mataki don kara samar da kayan gona.
Bugu da kari, Kim ya bayyana cewa za su ci gaba da aiwatar da matakan kulle don dake yaduwar Korona duk da matsalolin Tattalin arzikin da ake fuskanta.