Ma’aikatar tsaron Korea ta kudu ta ce da misalin ƙarfe 3 agogon GMT ne Korea ta arewa ta yi gwajin wanda ya nufi yankin gabashi jim kaɗan bayan ganawar Blinken da shugaban riƙo na ƙasar Choi Sang-mok.
Yayin ganawar Blinken ya baiwa Korea ta kudu cikakken ƙwarin gwiwar ci gaba da mara mata baya don kawar da duk wata barazana daga makwabciyar ta Korea ta Arewa.
Ziyarar ta Blinken na zuwa kwanaki ƙalilan gabanin ƙarewar wa’adin mulkin Biden kan kujerar shugabancin Amurka.
Gwajin makamin mai cin matsakaicin shi ne karon farko da Korea ta Arewa ta yi tun bayan makamancinsa a ranar 5 ga watan Nuwamban bara lokacin da ta harba manyan makamai har guda 5 a lokaci guda ta kan ruwa.
Ma’aikatar tsaron ta Korea ta kudu ta ce ba ta da tabbacin nau’in makamin da makwabciyartata ta harba a wannan karon.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI