Kongo ce kasar da aka fi samun yawan mutanen dake fama da matsanancin yunwa a doron kasa

Kongo ce kasar da aka fi samun yawan mutanen dake fama da matsanancin yunwa a doron kasa

A yayinda Majalisar Dinkin Duniya a shekarar 2018 ta bayyana cewa mutane miliyan 13 ke fama da matsalar rashin abinci a Jamhoriyar Demokradiyyar Kongo a shekarar bana yawan ya haura miliyan 27 kuma daya cikin mutun uku na fama da matsanancin yunwa.

Dangane ga binciken da Majalisar Dinkin Duniya ta gudanar a kasar Jamhoriyar Demokradiyyar Kongo ce aka fi samun yawan mutanen dake fama da matsanancin yunwa a doron kasa. 

Haka kuma dangane ga sharhin da Hukumar Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya (FAO) da Hukumar Shirin Abinci ta Duniya (WFP) suka gudanar na tabbatar da cewa a halin yanzu mutum miliyan 7 na fama da matsanancin yunwa da ka iya sanadiyar rayuwarsu. 

A kasashen da wadannan alumman ke neman agajin gaggawa rashin tsaro da rikice- rikice na daga cikin abubuwan da suke haifar da rashin abincin.

A kasar Kongo da annobar Korona virus da sauran cututtuka ke dada yaduwa lamarin ya kara munana. 


News Source:   ()