Dangantakar Amurka da Iran wacce aka yi tsanmanin za ta gyaru bayan zaben shugaban kasar Amurka da ya baiwa Biden nasarar hawa kan karagar mulki, hadi da kwan gaba kwan bayan tattaunawar yarjejeniyar nukiliya ya fara rikidewa zuwa rikice-rikice musanman a iyakokin Iraki da Siriya. A yayinda wakilin Iran ke neman farwa sansanonin Amurka, ita kuma Amurka na kaiwa dakarun dake da alaka da Iran farmaki kai tsaye. Ga dukkan alamu rikicin ruwan sanyi dake tsakanin kasashen biyu ka iya ta’azzara musanman akan lamurran kasar Siriya.
Akan wannan maudu’in mun sake kasancewa tare da Mal. Can ACUN manazarcin harkokin waje a Gidauniyar Nazarin Siyasa, Tattalin Arziki da Hallayar Dan Adam wato SETA…….
A lokacin mulkin Trump matakan Amurka akan Iran ya rinka karfafa sannu a hankali, lamarin da ya ta’azzara a karshe. Amurka ta fice daga yarjejeniyar nukiliya, ta kakkabawa Iran takunkumin tattalin arziki da kuma kin ba ta damar fitar da albarkatun mai zuwa kasashen waje. Bugu da kari, taimakawa dakarun dake kalubalantar Iran a iyakokin Iraki-Siriya-Yaman da kuma hadakar da Isra’ila ta yi da kasashen yankin gulf sun kara matsin lamba ga kasar Iran. Tare da kashe Kwamandan Rundunar Sojojin Kudus Kassim Sulaimani da kuma ramuwar gayyar da sojojin Iran suka yi, ya sanya kasashen biyu kusan gwabza yaki kai tsaye a tsakaninsu.
Ala kulli halin, da zaben Biden a matsayin shugaban Amurka, wannan ƙawancen da ke adawa da Iran ya wargaje, kuma manufofin Amurka kan Iran sun yi laushi. Biden ya sake farfado da yarjejeniyar nukiliyar da Iran lamarin da ya nuna wata farar fata tsakanin kasashen biyu. Haka kuma ficewar Amurka daga tallafawa yakin da ake yi a Yamen shi ma ya karfafa wannan halin.
Sai dai; halin rashin daidaituwa na bangarorin da toshe tattaunawar nukiliya ya sanya rikici tsakanin ƙasashen biyu ya fara ƙaruwa. Lamarin ya kara gurbata sanadiyar rokon da Isra’ila ke yiwa Amurka akan daukar wasu matakai a yankin gulf. A karshe dai, bangarorin biyu sun fara kalubalantar juna musanman a yankunan Iraki. 'Yan kungiyar Shi'a ta (Hashd al-Shaabi) da ke aiki a karkashin kulawar Iran sun fara kai hari kan sansanonin Amurka da kuma akan jerin gwanon motocin jami’an Amurka a yankin. Wurare irin su sansanin sojin saman Amurka dake Erbil da na Ayn al-Assad Military Base, ana yawan kai hare-hare da makamai masu linzami da kuma da jiragen sama masu dauke da bam.
Dakarun Amurka kuwa sun fara mayarwa da ‘yan Shi’an dake yankin martani ta hanyar kai farmakai ta sama da bama-bamai. Wannan yakin ruwan sanyin dake tsakaninin kasashen biyu ya fara yaduwa zuwa kasar Siriya. Mayakan Iran sun kai hari kan sansanin Amurka a yankin rijiyar mai na El Omar da ke gabashin Deir Ezzor da wani jirgi mara matuki. Ita kuwa Amurka ta kai farmaki da bam akan sansanin ‘yan Shi’an dake yankin Elbu Kemal.
Gaskiyar tambaya anan ita ce- ko ɓangarorin za su gwammace su faɗaɗa waɗannan rikice-rikicen ko kuma a’a. Yayin da dukkan bangarorin ke daukar matakai don karfafa hannayensu a tattaunawar nukiliya, ba sa jinkirin jibge sojojinsu a filin daga. Wahalar wacannan tabi’ar akan kasashe kamar su Irak da Siriya ne yake karewa. A lokacin da Amurka ta fara janye sojojinta daga Gabas ta Tsakiya sannu a hankali, lamari ne da zai iya karawa Iran karfin gwiwa. Sai dai kuma bai kamata a manta da cewa Isra’ila da kasashen yankin gulf ka iya rufe gurbin da Amurkan za ta bari ba.
Wannan sharhin Mal. Can ACUN ne manazarcin harkokin waje a Gidauniyar Nazarin Siyasa, Tattalin Arziki da Hallayar Dan Adam wato SETA dake nan Ankara babban birnin Turkiyya.