A yayinda aka mance da juya halin Larabawa, abin bakin ciki ne yadda yakin basasan Siriya ya cika shekaru goma ana aikatawa. A yayinda kusa da rabin al’umman kasar suka rasa matsugunansu; kusan mutum miliyan daya sun rasa rayukansu. Hakikanin gaskiya kasar ta fuskancin munanan yanayi na kin kari. Shin ko hanyar siyasa za ta iya kawo karshen matsalar kasar?
Akan wannan maudu’in mun kasance tare da Mal Can Acun manazarcin harkokin waje a Gidauniyar Nazarin Siyasa, Tattalin Arziki da Hallayar Dan Adam wato SETA….
Juya juya halin kasasshen Larabawa da ya fara a kasar Tunisiya, ya tattaro talakawa wadanda suka kasance cikin mawuyacin hali da zummar kalubalantar shugabanin maso mulkin kama karya, yunkurin da ya fara habbakar da yawa daga cikinsu. Baya ga Tunisiya sai kuma yunkurin ya ci gaba a Misira. Sai dai lamarin a Siriya ya rinka sauyawa inda kasar ta fada cikin yakin basasa sannu a hankali. Hakan ya kasance sabili da yadda Rasha da Iran suka goyi bayan gwamnatin Bashar Asad yayinda al’umman kasar suka kalubalanceta. Acikin tsawon lokaci kuma tare da hadin bakin kungiyoyin leken asirin wasu kasashen kungiyoyin ta’addanci kamarsu Deash sun samu damar kame yankuna a kasar. Kasancewar yadda kasashen yamma suka janye da hadaka da masu adawa da gwamnatin Asad a kasar ya baiwa gwamnatin kasar da kasashen dake goyon bayanta kamar su Rasha da Iran samun karfin gwiwa.
A karshe dai, da taimakon da Turkiyya ke baiwa ‘yan adawan kasar ne ya basu damar tsayuwa a yankunan Idlib da kuma rike wasu yankunan da suka kubutar. Matakan da Turkiyya ta dauka a wadanan wurare ya sanya rage masifu akan al’umman dake yankunan.
Duk da haka a yankin gabashin Firat hadakar Amurka-PKK na ci gaba da ikon yankin. A halin yanzu dai kai kace ana kusa da raba kasar gida uku ne. Yakin basasan dai na rusa sassan kasar da dama. Kusan rabin al’umman kasar Siriya sun rasa matsugunansu, daya bisa ukunsu na neman mafaka a wasu kasashe. Tattalin arzikin kasar ya tabarbare ta kowace fuska, ga kuma matsalar rashin abinci. Ginukan kasar duk an kusa rusa su sabili da hare-haren kin karin da aka rinka kaiwa a kasar.
A yayinda ake ganin ire-iren wadannan fotonan Siriya na bacin rai akan abubuwan da suka faru cikin shekaru goma, ana kuma cigaba da tattaunawar samawa kasar mafita ta hanyar siyasa. Musanman yarjejeniyar Astana da Turkiyya, Rasha da Iran suka kaddamar nada muhinmanci wajen kafa kundin tsarin mulkin kasar. Sai dai kawo yanzu babu wata takaimammiyar matsaya da aka cimma. Gwamnatin kasar da ‘yan adawa babu wani matakin kirki da suka dauka na kawo karshen matsalolin dake tsakaninsu ko wani bangare dai na yunkurin samawa kansa wajen zama ne kawai. A kan hakan ne kuma sassan kungiyar ta’addar PKK wato PYD/YPG a Siriya ke kokarin baje kolinta a gabashin Firat. Sabili da haka a ko wace fannin dai ana iya bayyana cewa babu wani ingantaccen matakin kawo karshen matsalar kasar.
Wannan sharhin Mal Can Acun ne manazarcin harkokin waje a Gidauniyar Nazarin Siyasa, Tattalin Arziki da Hallayar Dan Adam wato SETA dake nan Ankara babban birnin kasar Turkiyya….Ku huta Lafiya.