Ko yaya mukabala tsakanin Sheik Abduljabbar da malaman Kano ta kaya?

Ko yaya mukabala tsakanin Sheik Abduljabbar da malaman Kano ta kaya?

A yau ne dai ma'aikatar dake kula da harkokin addini ta jihar Kano ta bayyana a matsayar ranar da za'a zauna mukabala da Malam Abduljabbar Kabara da wasu malaman Kano sakamakon korafe-korafen da suka sanya dakatar dashi daga yin wa'azi a watannin baya.

An dai fara zaman ne da safe amma a karshe an bayyana cewa Malam Abduljabbar bai bayar da amsar ainihin amsoshin da aka tambayeshi ko kafa hujja daga littafan da ya dogara akansu ba.

Inda kuma shi Malam Abduljabbar ya yi korafi akan tsarin da aka yi mukabalan inda yake cewa tsarin yi masa tambaya a cikin minti biyar ya kuma amsa a cikin minti goma da kuma rashin bayar da dama ga 'yan bangarensa su dauki bidiyon mukabalar bai dace ba.

A yayinda da Malam Abduljabbar ya bayyana cewa Malaman sun kasa musunta ko karyata Hadisan da yake cewa Bukhari ya rawaito da kuma cewa ba'a yi masa adalci a mukabalar ba; Malaman da suka kalubalanceshi sun ce ya kasa amsa mafi yawan tambayoyin da suka yi masa.

Malam Kabara dai ya zargi ma'aikatar harkokin addini da sauya tsarin mukabalar sabanin yadda aka shirya za'a gudanar da ita a baya.


News Source:   ()