Ko ya kamata a yiwa yara allurar riga-kafin Korona?

Ko ya kamata a yiwa yara allurar riga-kafin Korona?

Amurka ta bi sahun Kanada da Algeria da suka fara bayar da izinin fara yin allurar riga-kafin Pfizer da BioNTech ta COVID-19 ga yara ƙanana masu shekaru daga 12. Hakan ya biyu bayan tabbacin da Hukumar Abinci da Magunguna (FDA) ta yi akan iya yiwa yara alluarar

Haka kuma  kanfanin Pfizer ta bayyana cewa ta mika bukata ga hukumomin kula da kiwon lafiya da suka hada da Hukumar Kula da Magunguna ta Turai (EMA) domin bayar da izinin fara yiwa yara kanana allurar riga-kafin.

Hukumar FDA ta bayyana cewa alluarar Pfizer ba ta da wata matsala ga yara, sanarwar ya biyu bayan gwajin da suka yi akan yara dubu 2,260 wadanda rabi daga cikinsu an yi musu allurar riga-kafin da ake yiwa manya ne, sauran rabin kuma aka yi musu allurar samfarin Placebo domin a iya kamantawa.

An gano cewa ingancin maganin ya kasance dai-dai akan yara ‘yan shekaru 12 -15 da ‘yan shekaru 16-25.

Dan nakasun da aka fi samu wanda basa jimawa sun hada da jin zafi a inda aka yi alluarar, gajiya, ciwon kai, ciwon gabobi da zazzabi. Hukumar FDA ta bayyana cewa fiye da yara miliyan 2 ‘yan tsakanin shekara 16-17 sun karbi allurar riga-kafin Pfizer-BioNTech.

 


News Source:   ()