Ko ya dangantakar Amurka za ta kasance da China a mulkin Biden

Ko ya dangantakar Amurka za ta kasance da China a mulkin Biden

An bayyana cewa an samu sabanin ra’ayi a zaman da bangarorın Amurka da China suka yi akan tsare-tsaren dangantakar kasashen biyu.

Amurka dai na bayyana cewa za ta tattauana da China akan harin yanar gizon akan Amurka da kuma matakan da China ta dauka akan Xinjiang, Hong Kong, da Taiwan kaman yadda sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya shaidawa takwaransa na China.

Ya kara da cewa dukkanin wadanan matakai sun sabawa dokar kasa da kasa wadanda ka iya dagule tsanakin kasa da kasa.

Gwamnatin Biden dai ta yi nuni da cewa ta na bukatar China ta sauya salonta da dabi’unta ta yarda huldan kasashen biyu zai gyaru wanda ya tabarbare karkashin mulkin Donald Trump.

Wani babbab jami’in diflomasiyyar China kuwa ya mayar da martani inda yake kalubalantar tangadin demokradiyyar Amurka, rashin adalci ga marasa riinjaye da kuma rashin tsakanin tsaron kasuwancinta na kasa da kasa.

Yang ya kara da zargin Amurka akan amfani da damar da take dashi wajen kalubalanta da takurawa wasu kasashe.


News Source:   ()