Da yawan al’umma na damuwa kwarai da gaske akan tunanin cewa ko bayar da tazara da nisantar juna ka iya rage karfin garkuwar jikkin biladama sabili da nisanta kai da juna a lokacin Covid-19 tamkar nisanta kai daga wasu kwayoyin halitta ne.
Masana sun bayyyana cewa wannan ba wani abin damuwa bane, sabili da ko a gida mutum kan kasance kusa da wasu kwayoyin halittan da garkuwar jikinsa za ta iya sabawa dasu.
Akiko Iwasaki, masanin garkuwar jikin dan adam a jami’ar Yale ya bayyana cewa jikin bil adama ko da yaushe yana cin karo da kwayoyin cutar da yake fada dasu kuma allurar riga-kafin da aka yiwa mutum tun yana yaro suna jimawa suna aiki a jikkinsa sabili da haka nisantar juna a wannan lokaci na Korona ba zai rage wa garkuwar jikin mutum karfi ba.