An sanar da rasuwar mutane 19 sanadiyar rikice rikicen kabilanci har biyu da suka afku a jihar Gombe dake kasar Najeriya.
Kamar yadda kafafen yada labaran kasar suka rawaito a yankin Lunguda da Waja rikicin kabilanci ya haifar da mutuwar wasu karin mutane hudu.
Akan haka mutane 19 suka rasa rayukansu a rikicin yankin.
Haka kuma rikicin ya haifar da konewar gidaje da dama da kuma sanya daruruwan mutane kaura daga matsugunansu.
Tuni dai an saka dokar hana fita waje bayan rikicin a jihar.
Wasu masu sharhi na bayyana cewa rashin raba albarkatun yankin bisa daidaito na daya daga cikin abubuwan da suke haifar da rikice rikicen kabilanci a jihar ta Gombe dake kasar Najeriya.