Ko me ake nufi da allurar rigakafin COVID-19 ta na da tasirin kashi 95 cikin dari?

Ko me ake nufi da allurar rigakafin COVID-19 ta na da tasirin kashi 95 cikin dari?

A yayinda kasashen a fadin duniya suka fara  mayar da hankali akan allurar riga-kafin Covid-19 kanfuanan da suka samar da ita na bayyana cewa allurar za ta yi tasirin kaso 90 cikin dari. Ko hakan na nufin mutum tara cikin goman da aka yi wa allurar ba zasu kamu da cutar ba?

Biyu daga cikin kanfunan da suka sarrafa allurar riga-kafın sun bayyana gwaje-gwajen da suka yi ya nuna cewa allurar da suka samar nada tasiri kwarai da gaske. A makon jiya Moderna ta bayyana cewa allurar riga-kafin Covid-19 da ta samar yana da tasirin kashi 95 cikin dari. Kanfanin Oxford/AstraZeneca kuwa ta bayyana cewa allurar riga-kafin ta nada tasirin kashi 70 cikin dari wanda kuma zai iya kaiwa kashi 90, su ma kanfunan Pfizer da BioNTech sun sanar da cewa allurar da suka samar suna da tasiri kwarai da gaske kamar na sauran kanfunan.

Wadanan alkaluma dai sun farantawa duniya rai akan ganin cewa za a iya magance annobar ba tare da jimawa ba. Sai dai wadannan alkaluman lamban me suke nufi?

Allurar riga-kafi dai na nufin rage yaduwar cuta tsakanin wadanda aka yiwa fiye da wadanda ba a yiwa ba. Kamar yadda Dkt. Shelly McNeil na Cibiyar Yaki da Yaduwar Cuttutuka dake Kanada ta sanar,  akan tabbatar da tasirin allurar  riga-kafi ne ta hanyar gwaje-gwaje kuma ta hakan ne kamfunan suka tabbatar da alluran da suka samar nada tasirin kaso 95 cikin dari.

Sai dai McNeil ta yi sharhin cewa tasirin allurar riga-kafi ya ta’alaka ne akan karfin rage kamuwa da yaduwar cutar a cikin al’umma, ta yi wannan sharhin ne a taron Hukumar Lafiya ta Duniya wato WHO.

A gefe guda kuma jaridar Daily Sabah ta rawaito cewa ana fargaban allurar riga-kafin Korona za ta yi tasiri ne tamkar na mura wacce tasirinta bai wuce kaso 20-60 cikin dari kawai ba.

Sai dai kuma an tabbatar da cewa idan aka yiwa mutane da dama allurar riga-kafi yaduwar cutar da take kalubalnata zai  ragu kwarai da gaske.


News Source:   ()