An bayyana cewa akwai yiwuwar kwayar cutar Korona na yaduwa a tsakanin yara sai dai sauri da yawan yaduwar zai iya kasancewa akan shekarunsu.
Binciken da jaridan Daily Sabah ta yada ya nuna cewa yara ‘yan kasa da shekaru 10 basu cika saurin yada cutar ga ‘yan uwansu yara da manya ba kamar wadanda suka dara hakan.
Yara dai basu cika rashin lafiya ba ko da sun kamu da cutar ta Korona, haka kuma ma basu cika bayyana alamun suna dauke da ita ba kaman manyan mutane. Binciken ya kara da cewa yara kanana basu cika yada cutar ba saboida basu cikin yin tari ko atashawa ba koda suna dauke da cutar.