Wani masanin diflomasiyya dan kasar Jordan ya yi kira ga Isra’ila da ko dai ta zabi zaman lafiya ko kuma ta zabi ci gaba da kasancewa cikin rikici.
Ya yi wannan kiran ne a yayinda yake sharhi akan yarjejeniyar sulhun da Hadaddiyar Daular Larabawa ta yi da Isra’ila
Ministan harkokin wajen Jordan Ayman al-Safadi ya bayyana cewar tasirin yarjejeniyar ya ta’alaka ne akan irin matakan da Isra’ila zata dauka a yankin.
Ya kara da cewa "Idan Isra’ila ta amince da dakatar da mamayar da take yi ta mayar wa Falasdinawa hakkokinsu yadda zasu kafa kasarsu bisa da yadda taswirarsu yake a shekarar 1967 da gabashin Jarusalam a matsayar babban birnin kasar, yankin zai kasance cikin lumana. Amma idan Isra’ila bata amince da hakan bar ikici zai kara kamari a yankin”