Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta sanar da cewa za'a iya fara tabbatar da cewa dabbobi ka iya yada kwayar cutar Covid-19 idan aka tabbatar da wani bincike da ake yi a wani gidan gona dake Netherland.
Hukumar WHO ta sanar da cewa ana cigaba da binciken hakan a wani gidan gonan da ake kiwon dabbar mink domin samun gashin jikinsu. Ana hasashen cewa ma'iakata biyu a gidan gonan sun kamu da kwayar cutar corona daga dabbobin.
Hukumar WHO ta bayyana cewa idan aka tabbatar da hasashen zai kasance tabbaci na farko da cewa mutane ka iya daukar cutar daga dabba.
A farkon bulluwar kwayar cutar an bayyyana cewa za'a iya daukar cutar ne daga iska da kuma ganawa da mutane amma ba daga dabbobi ba.