Ko Amurka za ta bai wa Ukraine izinin amfani da makaminta kan Rasha?

Ko Amurka za ta bai wa Ukraine izinin amfani da makaminta kan Rasha?

Matakin na zuwa ne bayan ziyarar farko da Firaministan Birtaniya Keir Starmer ya kai fadar White House ta Amurka, yayin da ake ci gaba da murza gashin baki kan batun na amfani da makaman Turai.

Tuni Birtaniya ta ayyana nata shirin da bai wa Ukraine cikakkiyar damar da take buƙata na matsawa Rasha da hare-hare ta yadda za ta samu damar kwato guraren da dakarun Rasha suka kwace.

Ukraine dai na buƙatar cikakkiyar dama a hukumance daga Amurka don fara amfani da makaman daga nan kuma sai sahalewar ƙasar Faransa.

Manyan jami’an gwamnatin Amurka sun ce har kawo yanzu Joe Biden bai bada umarnin a hukumance ba, amma dukannin alamu da kalamansa sun nuna cewa ya kammala shirin sahalewa.

Kwararru kan dubarun yaƙi na ganin cewa Mr. Biden na jan kafa ne don gudun abin da kaje ya zo, kasancewar ba makawa Rasha za ta mayar da martani lamarin da ke nuna cewa kai tsaye Amurka ta shiga yaƙin, watakila kuma ta samu tallafin Iran ta hanyar kai wa dakarunta da ke Gabas ta Tsakiya hari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)