A yayinda ake cigaba da yin allurar riga-kafin Korona a fadin duniya masoya harkokin wasanni na ci gaba da tambayar cewa: Ko babu hadarin kamuwa da cutar Korona a filayen wasanni kamar na kwallon kafa da na kwando.
Kawo yanzu dai babu takaimayyiyar amsa akan tambayar domin masana na ci gaba da gudanar da bincike akan lamarin.
Amma sun bayyana cewa rera take kungiya, wakoki da rumguman juna a filayen wasanni akwai hatsari a aikatasu domin za’a iya daukar cutar Korona a wannan lokacin., hakan ya fito bakin Ferfesa Jennifer Dowd na harkokin kiwaon lafiyar al’umma dake jami’ar Oxford ne
Ya kara da cewa filayen wasannin dake bude sun fi rashin hadarin kamuwa da kwayar cutar Korona, fiye da wadanda ke rufe, duk da ko wasu kungiyoyi na bukatar al’umma su nuna alamar an yi musu allurar riga-kafin Korona gabanin su shiga filin wasa.
Ya kara da cewa idan mutane su ka rinka cin abinci da shan abin sha a yayin da suke kallon wasanni, hadarin kamuwa da Korona zai kara yawa.