
Sama da shekaru dubu biyu ke nan mabiya addinin Kirista suka kwashe suna gudanar da wannan biki a duk fadin duniya, ta hanyar nuna farin ciki da ƙauma da tausayin juna da sadaukarwa da dai sauransu.
A Bethleham mahaifar Yesu Kiristi da ke cikin yankin Falasɗinawa, inda daruruwan mutane ke kai ziyara a irin wannan lokaci a shekarun baya, a bana ya kasance shiru, sai dai da dama daga cikin waɗanda suke a yankin sun mai da hankali ne wajen yiwa waɗanda hare-haren Isra’ila ya hallaka a yankin Gaza addu’a.
A jawabin da Fafaroma Francis ya gabatar a majami’ar Saint Peter’s Basilica ya yin taron jajibirin Kirsimeti, ya ja hankalin Kiristoci da su yi tunanin game da yaƙe-yaƙen da ake fama da su a sassan duniya, yayin da a bana ma ake gudanar da bukukuwan Kirsimeti cikin yaƙin Isra’ila da Hamas da kuma Rasha da Ukraine.
Kalaman nasa na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan da ya yi Allah wadai da mummunar hare-haren da Isra'ila ke kai wa, wanda jami'an diflomasiyyar Isra'ila suka yi watsi da su.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI