Kiristoci sama da biliyan biyu a faɗin duniya na gudanar da bikin Kirsimeti

Kiristoci sama da biliyan biyu a faɗin duniya na gudanar da bikin Kirsimeti

Sama da shekaru dubu biyu ke nan mabiya addinin Kirista suka kwashe suna gudanar da wannan biki a duk fadin duniya, ta hanyar nuna farin ciki da ƙauma da tausayin juna da sadaukarwa da dai sauransu.

A Bethleham mahaifar Yesu Kiristi da ke cikin yankin Falasɗinawa, inda daruruwan mutane ke kai ziyara a irin wannan lokaci a shekarun baya, a bana ya kasance shiru, sai dai da dama daga cikin waɗanda suke a yankin sun mai da hankali ne wajen yiwa waɗanda hare-haren Isra’ila ya hallaka a yankin Gaza addu’a.

Sama da shekaru dubu biyu ke nan mabiya addinin Kirista suka kwashe suna gudanar da bikin Kirsimati a duk fadin duniya. Sama da shekaru dubu biyu ke nan mabiya addinin Kirista suka kwashe suna gudanar da bikin Kirsimati a duk fadin duniya. © Pierre Olivier / RFI

A jawabin da Fafaroma Francis ya gabatar a majami’ar Saint Peter’s Basilica ya yin taron jajibirin Kirsimeti, ya ja hankalin Kiristoci da su yi tunanin game da yaƙe-yaƙen da ake fama da su a sassan duniya, yayin da a bana ma ake gudanar da bukukuwan Kirsimeti cikin yaƙin Isra’ila da Hamas da kuma Rasha da Ukraine.

Jagoran mabiya darikar Katolika Fafaroma Francis. Jagoran mabiya darikar Katolika Fafaroma Francis. © AFP/VATICAN MEDIA

Kalaman nasa na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan da ya yi Allah wadai da mummunar hare-haren da Isra'ila ke kai wa, wanda jami'an diflomasiyyar Isra'ila suka yi watsi da su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)