Ministan Harkokin Wajen Katar, Mohammed bin Abdurrahman Al Sani ya gayyaci kasashen Larabawa na Gulf don tattaunawa da Iran kuma ya bayyana cewar Katar za ta iya sasanta tsakani a wannan tattaunawar.
A bayanansa ga gidan talabijin na Bloomberg, Al Sani ya sake nanata kiransa ga mambobi 6 na Majalisar Hadin Kan Gulf (GCC) kan tattaunawa da Iran.
Ya ce ”Gwamnatinmu na fatan cewa za a gudanar da wannan tattaunawar kuma tana ganin ya kamata hakan ya faru."
Da Al Sani ya ke nuni da cewa kasashe mambobin GCC suma suna sai rai kan afkuwar tattaunawar kamar su, ya kuma ce Katar a shirye take ta sasanta idan hakan ya zama dole.
Al Sani, dangane da yiwuwar fara tattaunawa tsakanin Amurka da Iran, ya ce
“Katar za ta iya shiga tsakani a tattaunawar idan wani mai ruwa da tsaki ya nema. Muna son samun nasara, za mu so ganin yarjejeniya tsakanin Amurka da Iran."