kimanin mutane 307,433  suka kamu da cutar kwalara daga ciki mutane 2,326 sun mutu-WHO

A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a ranar alhamis ta ce yankunan da aka samu barkewar cutar ta Cholara sun hadar da  yankin Afirka da yankin kudu maso gabashin Asiya da yankin Amurka da kuma yankin Turai.

 

Matsalar cutar ta kwalara na ci gaba da yin kamari bayaga  matsanancin karancin alluran rigakafin ta, kawo yanzu a kalla kasashe 18 suka nemi allurai miliyan 105 tun daga watan Janairun 2023.

 

Hukumar ta dauki matakin samar da allurar rigakafin ce a wani yunƙuri na daƙile cutar cikin gaggauwa a watan Junairu.

 

Kasashe irin su  Najeriya na cikin kasashen da suka fuskanci annobar cutar ta kwalara a wasu daga cikin manyan jihohinta wanda tuni gwamnatin kasar ta dauki matakan daƙile ta..

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)