A Senegal, mutane 11 sun rasa rayukansu sakamakon nutsewar jirgin ruwan da ke dauke da wadanda ke son tsallakawa ba bisa ka'ida ba zuwa Spain.
A cikin sanarwar da sashin yada labarai na rundunar sojojin Senegal ya fitar, an bayyana cewa kwale-kwalen da ke dauke da wadanda suka tashi zuwa tsibirin Canary na Spain ba bisa ka'ida ba ya kife a gabar tekun birnin Saint-Louis, kilomita 250 daga Dakar, a daren 25 ga Agusta zuwa 26 ga Agusta.
An ba da rahoton cewa akwai mutane 60 a cikin kwale -kwalen, wanda ya kife da tazarar kilomita 35 daga kogin Senegal, kuma ya zuwa yanzu an gano gawarwakin mutane 11, wadanda 8 daga cikinsu 'yan Senegal ne kuma 3 daga cikinsu' yan Gambiya.
A cikin sanarwar, an bayyana cewa kungiyoyin kare hakkin farar hula na Spain suma sun shiga aikin bincike da ceto.