An samu hasarar rayukan 'yan gudun hijira 14 sakamakon kifewar wasu kwale-kwale biyu a yankin garin Sfaks dake kasar Tunisiya.
Kamar yadda kanfanin dillacin labaran Tunisiya ta TAP ya rawaito, mai magana da yawun rundunar 'yan sandan kasar Husameddin Al -Jibali ya bayyana cewa kwale-kwale biyu sun kife dauke da 'yan gudun hijira daga kasashen Afirka.
Jibali, ya kara da cewa bakin hauren na kan hanyarsu ta zuwa kasashen Nahiyar Turai ne inda daga cikinsu aka samu hasarar rayukan mutum 14 da sukja hada da yara 4 da mata 9.
Jibali, ya tabbatar da cewa a cikin kwale-kwalen na farko akwai mutum 46 na biyu kuwa mutum 94 wadanda aka kubutar a yayinda ake ci gaba da neman sauran.