An kashe jami'an tsaro 5 da 'yan tawaye 2 sakamakon kazamin rikicin da suka fafata a jihar Haybar Pahtunhva da ke Pakistan.
Kakakin 'yan sandan jihar Imtiaz Han ya ce an samu arangamar a lokacin da jami'an tsaron suka kai farmaki wani gida da ke yankin Chilas na iyaka da Afganistan.
Han ya kara da cewar an kashe jami'an tsaro 5, an kuma kashe 'yan tawaye 2 tare d jikkata 4 a rikicin.
Ba a bayyana ko 'yan wacce kungiya ba ne 'yan tawayen da aka kashe.