Kazamin harin bam ya kashe musulmi ƴan ƙabilar Rohingya 41 a Myanmar

Kazamin harin bam ya kashe musulmi ƴan ƙabilar Rohingya 41 a Myanmar

Da tsakar ranar Laraba ne jiragen saman sojin Myanmar sun yi ɓarin bama a ƙauyen Kyauk Ni Maw da ke gabar Ramree, matakin da yayi sanadiyar haifar da gobarar da ta lakume gidaje akalla 600, ya kuma turnuke sararin samaniya da hayaki kamar yadda mazauna yankin suka tabbatarwa manem alabarai.

Yankin dai na karkashin ikon wadanda ke adawa da gwamnatin sojin kasar wato Arakan, kuma a cewar kakakin su Khaing Thu Kha , har zuwa lokacin da aka kai harin saman, babu wata fada da ta barke.

Yayin zantawarsa da manema labarai, Khaing Thu Kha ya ƙara da cewa ci gaba da kaiwa waɗanda basu ji ba basu gani ba hari, musamman a yankunan da ba a fama da rikici tsantsar zalunci ne da kuma nuna ragontaka.

To sai dai a ta bakin kakakin sojin gwamnatin kasar da ke jihar Rakhine, Hla Thein, ba shi da masaniya a game da faruwar lamarin, duk kuwa da taimakon gaggauwa da masu kiwon lafiya ke kaiwa waɗanda suka jikkata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)