Kazakhstan ta taimakawa Turkiyya kashe gobarar daji

Kazakhstan ta taimakawa Turkiyya kashe gobarar daji

Kasar Kazakhstan ta aike da jirage masu saukar ungulu samfurin MI-8AMT 2 da tawagar kashe gobara ta musamman da ya kunshi mutane 16 zuwa Turkiyya domin yaki da gobarar daji.

A cikin sanarwar da Ma’aikatar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kazakhstan ta fitar, an ba da rahoton cewa jirage masu saukar ungulu 2 da wata tawaga ta musamman da ke da alaka da ma’aikatar sun tashi zuwa Mugla don tallafawa yaki da gobarar daji, bisa umarnin Shugaba Kasım Comert Tokayev.

Sanarwar ta kuma lura cewa Kazakhstan a shirye take ta ba da taimakon jin kai don maido da gandun daji da gobara ta lalata.


News Source:   ()