Kazakhstan ta yanke shawarar kara yawan zirga-zirgan jiragen dake zuwa Antalya daga 7 ga watan Yuni har sau 8 a kowane mako.
A cewar sanarwar da Ma'aikatar Masana'antu da Ci Gaban Kazakhstan ta fitar, bisa ga sabon shawarar da Hukumar Gwamnati ta yanke kan sabon nau'in kwayar Coronavirus (Kovid-19), yawan jirage da ke zuwa Turkiyya da Uzbekistan za su karu.
daga ranar 7 ga Yuni, kamfanonin jiragen sama za su yi zirga-zirga sau 8 a kowane mako daga Kazakhstan zuwa Antalya.
Bugu da kari, za a bude jiragen na yau da kullun zuwa biranen Namangan, Nukus da Samarkand na Uzbekistan.
Ministan Masana'antu da Bunkasa Kayan Kazakhstan Beibut Atamkulov a baya ya bayyana cewa adadi mai yawa na 'yan kasar sun zo Turkiyya hutu a watannin bazara kuma suna tattaunawa don kara yawan jiragen da za su tashi zuwa Antalya, tare da yin la'akari da wannan halin da ake ciki na yaki da Korona.