Kayan taimako da Turkiyya ta aika Tunisiya sun isa birnin Tunus

Kayan taimako da Turkiyya ta aika Tunisiya sun isa birnin Tunus

Jirgin saman daukar kaya dauke da kayan taimakon da Turkiyya ta aika zuwa Tunisiya ya isa filin tashi da saukar jiragen sama na Kasa da Kasa na Kartaja da ke  Tunus Babban Birnin Kasar.

Jakadan Turkiyya a Tunus Ali Onaner ya fitar da sanarwa ta shafinsa na Twitter cewar sun tarbi kayan da jirgin daukar kaya na kamfanin jiragen saman Turkiyya Turkish Airlines mafi girma samfurin B777330 ya dauka zuwa Tunus.

Onaner ya ce a amakon da ya gabata ma an mika wasu kayan taimakon ga yankin jerbe na kudancin Tunisiya.

Ya ce "Tare za mu yi nasara kan cutar." inda ya kara da cewar Turkiyya ta ci gaba da taimakawa Tunisiya don yaki da Covid-19.

Kasar Falasdin ma ta karbi kayan taimakon yaki da annobar Corona (Covid-19) da Turkiyya ta aika mata.

A wajen taron mika kayan da aka gudanar a garin Ramallah na Yammacin Gabar Kogin Jordan da Yahudawa suka mamaye, Ministan Harkokin Wajen Falasdin Riyad Al-Maliki, Jakadan Turkiyya a Kudus Ahmet Riza Demirer da sauran mahukuntan Falasdin sun samu damar halarta.

Minista Al-Maliki ya bayyana cewar wannan taimako da aka ba kasarsu don ci gaba da yaki da Corona na da matukar muhimmanci, kuma suna mika godiyarsu ga Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan.

Ya ce "Wannan taimako na nuni da irin kyakkyawar alakar da ke tsakanin Shugaban Falasdin Mahmud Abbas da Shugaba Erdogan na Turkiyya."

A ranar 30 ga Afrilu ne jirgin saman daukar kaya na Turkiyya dauke da kayan taimako ga Falasdin ya isa filin tashi da saukar jiragen sama na Gurion da ke kusa da Tel Aviv Babban Birnin Isra'ila.

A baya ma Turkiyya ta aike da kayan taimako don yaki da annobar Corona Covid-19 a kasashen Somaliya, Falasdin, Amurka, Italiya, Spaniya, Kosovo, Makedoniya, Sabiya, Bosniya, Ingila, Afirka ta Kudu, Indonesiya Uganda, Montenegro da sauransu.



News Source:   www.trt.net.tr