A ci gaba da yaki da kwayar cutar Covid-19 a Turkiyya a cikin awanni 24 da suka gabata mutum 15 sun rasa rayukansu.
Tun farkon bulluwar cutar a kasar kawao yanzu mtum dubu 5 da dari 813 ne suka rasa rayukansu a kasar.
A cikin rana daya an yiwa mutum dubu 56 da dari 726 gwajin kwayar cutar inda aka samu mutum dubu 1 da dari 185 dauke da ita.
Haka kuma wadanda suka warke a ranar sun kai dubu 1 da da 28, a jumlace wadanda suka warke daga cutar a kasar sun kai dubu 221 da dari 574.