A cigaba da yaki da kwayar cutar Covid-19 a Turkiyya a cikin awanni 24 da suka gabata mutum 69 sun rasa rayukansu.
Tun farkon bulluwar cutar a kasar kawo yanzu mutum dubu 9 da dari 727 ne suka rasa rayukansu a kasar.
A cikin rana daya an yiwa mutum dubu 113 da dari 427 gwajin kwayar cutar inda aka samu mutum dubu 2 da da 91 dauke da ita.
Haka kuma wadanda suka warke a ranar sun kai dubu 1 da da 573, a jumlace wadanda suka warke daga cutar a kasar sun kai dubu 313 da 93.