Kawo yanzu Covid-19 ta yi ajalin mutum miliyan daya da dubu 37 a doron kasa

Kawo yanzu Covid-19 ta yi ajalin mutum miliyan daya da dubu 37 a doron kasa

A fadin duniya kawo yanzu kwayar cutar Covid-19 tayi sanadiyar rayukan mutum miliyan daya da dubu 37 da dari 980, inda yawan wadanda suka kamu da cutar ya kai miliyan 35 da dubu 135 da dari 530, yawan wandanda suka warke kuma ya kai miliyan 25 da dubu 126 da dari 915.

A cikin awanni 24 da suka gabata a Indiya cutar ta yi ajalin karin mutum 940 inda yawan wadanda ta kashe a kasar suka kai miliyan 37 da dubu 812. An kuma samu karin mutum dubu 75 da dari 829 dauke da cutar inda yawan wadanda suka kamu da cutar ya kai miliyan 6 da dubu 549 da 373.

An dai fara Umrah a kasar Saudiyya inda aka dakatar da yin haka na watannin shida. A halin yanzu dai mutum dubu 4 da dari 850 suka rasa rayukansu inda mutum dubu 335 da dari 997 suka kamu da cutar a kasar.

A Nahiyar Afirka kuwa a cikin awanni 24 da suika gabata an samu cutar ta yi ajalin mutum dubu 36 da dari 399. A Nahiyar mutum miliyan daya da dubu 514 da 844 suka kamu da cutar. Kawo yanzu dai a nahiyar a Afirka ta Kudu ne aka fi samun wadanda cutar ta yi ajali inda mutum dubu 16 da dari 938 suka easa rayukansu, a Misira dubu 5 da dari 970 sai Morocco da dubu 2 da dari 293.

 


News Source:   ()