A fadin duniya kawo yanzu kwayar cutar Covid-19 tayi sanadiyar rayukan mutum dubu 879, inda yawan wadanda suka kamu da cutar ya kai miliyan 26 da dubu 795 da dari 850, yawan wandanda suka warke kuma ya kai miliyan 18 da dubu 907 da dari 700.
A Amurka inda a halin yanzu cutar tafi yin katutu Corona ta yi ajalin mutum dubu 192 da dari 111, yawan wadanda suka kamu da ita kuwa sun kai miliyna 6 da dari 389 da 57.
A Nahiyar Turai inda cutar ta yi ajalin mutum dubu 41 da dari 537, a cikin awanni 24 da suka gabata a Birtaniya an samu karin mutum dubu 1 da dari 940 dauke da cutar, a jumlace mutum dubu 342 da dari 351 ke dauke da ita a kasar. A kasar daga 8 ga watan Agusta zuwa 3 ga watan Satumba ana samun kimanin mutum 1 da 300 dauke da cutar ko wace rana.