Gwamnatin Amurka ta kwashe mutane dubu 105 daga Afghanistan tun daga ranar 14 ga watan Agusta da aka fara aikin kwashe mutanen.
A cewar wata rubutacciyar sanarwa daga Fadar White House, Amurka ta kwashe karin mutane 12,500 daga filin jirgin saman Hamid Karzai na Kabul a cikin awanni 24 da suka gabata.
A cikin awanni 24 da suka gabata, an kwashe mutane 8,500 da jiragen soji 35 sannan mutane 4,000 sun tashi da jiragen kawancen 54.
Don haka, an bayyana cewa adadin mutanen da Amurka ta kwashe tun ranar 14 ga Agusta, lokacin da aka fara aikin kwashe mutane, ya kai 105,000.
A gefe guda kuma an bayanai cewa adadin mutanen da aka kwashe daga Afghanistan tun daga karshen watan Yuli ya kai 110,600.